Sarkin Jama’are ya albarkaci wakata - Badariyya meke tsakaninta da AMINU BAGWAI HAR YAYI MATA WAKA?

“Godiya ga mutan Jama’are, Jama’are garin Badariyya!” Wakar da take ta tashe ke nan a sassan kasar nan har ma da kasashen waje. Amma wace ce Badariyya? Wakilinmu ya yi tattaki har zuwa garin Jama’are, inda ya gana da Badariyya, ta yi masa bayani filla-filla, yadda ta hadu da mawaki Aminu Bagwai, wanda kuma ya wake ta. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Ki gabatar da kanki ga masu karatu?

Sunana Badariyya A Jarma, wacce yanzu aka fi sani da Badariyya Jama’are. An haife ni a ranar 1 ga watan Maris, 1990 a Karamar Hukumar Jama’are da ke Jihar Bauchi.

Ko mene ne sanadiyyar haduwarki da Aminu har ya yi maki waka?

Lambar wayarsa na nema, da na samu sai na kira shi don ya yi mini karin bayani a kan wakarsa da ya yi ta ta’aziyyar wadanda suka yi hadari a jirgin ruwa, musamman da yake takaddama ta kaure a kan ko hakan ya faru ko a’a. Da na kira shi ne ya sanar da ni tabbas hakan ya faru, a nan na yi masa jaje. Daga nan sai ya tambaye ni ko ina da aure na ce masa a’a. Tun daga nan sai muka fara mutunci. Ana haka wata rana sai ya kira ni ya ce zai kawo mini ziyara, kasancewar a lokutan da muke waya da shi a baya na shaida masa ina zaune a Kano wajen kanin mahaifina ne, amma ni asalin haifaffiyar Jama’are ce kuma mahaifana suna Jama’are.
Bayan ya kira ni ya tambaye ni ko a wacce unguwa nake zama, sai na ce masa a ’Yankaba, Kwanar Dakata. Shi ne ya zo, muna hira ya tambaye ni yaushe zan je Jama’are? Na sanar da shi cewa mako mai zuwa zan je. Haka dai muka ci gaba da hira, daga baya ya tafi.
Ina Jama’are sai ga wayarsa nan ta shigo, bayan na dauka sai muka gaisa, daga nan sai ya ce mini yana so ya zo Jama’are. Sai na ce masa ga shi kuwa bikin kanwata ya kusa, ko zai bari sai lokacin bikin ya zo? Ya amince da hakan. Da lokacin bikin ya yi, ya zo, yayyena da sauran dangina suke je suka dauko shi, aka kawo shi masauki, aka yi masa goma ta arziki. Duk abin da ya mema sai da aka yi masa. A lokacin ana yawan kiransa a waya, idan batirinsa ya kare sai na cire layinsa na sanya a daya daga cikin wayata, sannan na sanya tasa a caji. A lokacin ba shi da wata waya mai kyau, kuma dama ina da waya biyu Nokia N-series da Itel, sai na ba shi Nokia da Itel din ya rike a matsayin wayoyinsa. Dalilina na yi hakan shi ne, a yanzu mutane kiwon mutum suke ba na dabba ba, ya kuma amince da hakan.
Ya ji dadin karrama shi da aka yi, ko lokacin da zai tafi sai da ya je ya durkusa ya gaida mahaifana, sannan ya yi masu godiya. Na nemi mota na zuba mai aka kuma dauke su har zuwa garin Kano, kasancewar ba shi kadai ya zo ba. Ko bayan sun isa Kano, sai da na kira shi na tambaye shi ko sun isa lafiya? Ya ce mini sun isa lafiya. A nan na nemi ya hada ni da mahaifansa, ya kuma hada ni da su muka gaisa. Daga nan muka ci gaba da mutunci.
Wata rana sai ya kira ni a waya, ya tambaye ni yaya sunan yayana sai na fada masa sunansa Sayyadi da kuma abokinsa wanda ake kira Ali (G. Mama). Ya tambaye ni lambarsu na kuma ba shi.
Ana haka sai wata rana ya kira ni, bayan na dauka sai yake ce mini duk lokacin da yayana ya shigo Kano to ya same shi a ‘Danladi Nasidi’ akwai sakon da zai ba shi ya kawo mini. Na fada wa yayana, aka yi sa’a washegari zai je Kano. Ya je suka hadu sai ya ba shi wakar da ya yi mini ta ‘Jama’are Garin Badariyya’ ya kawo mini, wato faifan CD guda 3 da kuma kaset din rediyo guda 3.
Bayan yayana ya dawo a lokacin babu wuta sai muka tayar da inji, ya sanya waka muka ji. Na ji ta yi dadi, na rika mamakin yadda ya yi mini waka. Washegari na tafi shagon kwamfyuta suka sanya mini a cikin wayata. Shi ne fa tun daga nan wakar ta rika yaduwa har zuwa yau.

Ko soyayya ta shiga tsakaninku bayan ya yi miki waka, tun da kafin wakar mutunci ne a tsakaninku?

Bayan ya yi mini waka sai da muka yi wata hudu ba mu yi waya ba, duk da cewar ina nemansa amma wayarsa ba ta shiga, shi kuma bai taba kirana ba tun bayan ya yi mini wakar. Daga baya da na fara samunsa idan na kira shi sai ya tambaya wace ce? Sai na ce masa Badariyya ce, sai ya ce ‘au ke ce?’ Sai na ce masa ‘e.’ Haka muka ci gaba, ba zai neme ni ba sai dai na neme shi. Daga nan sai na yi wa kaina kiyamul laili na rage kiransa, musamman ma da nake mace. Ya kamata a ce ya fi nuna damuwa da ni a kan yadda nake yi masa.
Ana haka sai aka sace mini wayata, shi ke nan na daina kiransa. Bayan na sake sayan waya sai na sanar da shi sabuwar lambata, sannan na na ce masa ya goge tsohuwar. Ya ce shi ke nan amma kuma bai taba kira na ba. Ni ma kuma sai na daina kiransa.
Sannu a hankali na gamu da wani a Kano, muka fara soyayya. Amma duk da haka wata rana sai da na kira Aminu na tambaye shi yaushe zai zo mu hadu? Sai ya ce mini uzururruka sun yi masa yawa. Haka na ci gaba da neman ya zo, amma sai ya ci gaba da yi mini yawo da hankali. Daga nan sai na hakura da shi.
Wata rana sai ya kira ni wai zai zo Jama’are, sai na ce masa ina Kano ya zo mu hadu a ’Yankaba. Can sai ya kira ni ya ce mini yana kan hanyarsa ta zuwa, amma kuma an kira shi don haka ba zai samu damar karasowa ba. Ban sani ba ashe ya kira yayana ya ce masa zai zo Jama’are, sai ya ce masa ai ina Kano, amma duk da haka sai da ya je Jama’are. Yana Jama’aren ne ya kira ni, bayan na dauka ya ce mini yana Jama’are na zo, sai na ce masa ai dama na fada maka ina Kano, shi ne ya shiga fada. Ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba. Na ba shi hakuri, amma ya nuna ransa ya baci.
Daga nan ba mu kara yin waya ba sai da aka sanya ranar da zan yi aure, sai na kira shi na sanar da shi zan yi aure a Kano, ya yi mini addu’a Allah Ya ba da zaman lafiya.
Akwai wakar ‘Jama’are Garin Badariyya’ ta bidiyo, ko ke ce wacce aka dauki wakar da ita?
Gaskiya ba ni ba ce, don haka kada masu kallo su yi tsamminin ni ce. Baya ga haka duk abin da ya kwatanta a wakar ba haka ba ne abin da ya faru tsakanina da shi, amma dai kusan hakan ne. Ban ma san ya yi na bidiyo ba sai a gari na gani.

An baza jitar-jitar cewa Sarkin Jama’are ya sanya an kama ki da kuma mahaifanki, ko mece ce gaskiyar maganar?

Duk jita-jita ce babu wanda ya kama ni ko mahaifana. Sarkin Jama’are tamkar mahaifi yake a gare ni. Ya san mahaifana. Babana shi ne Sarkin Kidan Jama’are, akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin mahaifana da Sarkin Jama’are (Allah Ya kara masa daraja da martaba). Mai martaba albarka ya sanya wa wakar ma.
An ce ’yan Jama’are sun sanya miki kahon zuka saboda an ce Jama’are garin Badariyya, maimakon garin Sarki Ahmadu?
A gaskiya haka ne, wadansu sun rika yi mini wani irin mugun kallo. Ban dauki hakan a matsayin komai ba face hassada wacce take taki ga mai rabo, wanda duk a sakamakon daukaka da na samu ne, tun da a da ba su yi mini haka ba sai da aka yi mini waka.
Ina so mutane su gane mawakin ba yana nufin Jama’are garina ne ba, ya yi yadda wakarsa za ta yi dadi ne. Kuma a ganina murna ya kamata duk wani dan Jama’are ya yi saboda an kara sanin garinsa, kasancewar a yanzu ana jin wakar a Nijar da Kamaru da Chadi da sauransu. Akwai wanda ya sanar da ni cewa ya ji wakar a Saudiyya.

Idan yanzu Aminu Bagwai ya nemi auren ki, za ki amince, kasancewar a yanzu aurenki ya mutu ?
(Dariya). A yanzu haka ya fitar da wata waka, yana cewa wai na yaudare shi. Ni dai na cika da mamakin ko ta yaya na yaudare shi. Batun idan ya zo neman aurena ba zan iya cewa komai ba, saboda komai na duniya mukaddari ne daga Ubangiji, Shi ne mai tsara yadda Ya so a lokacin da Ya so, idan Allah Ya kaddara hakan ni ko Aminu babu mai iya tsallakewa. Allah Ya yi mana zabi na alheri.

Comments

Popular posts from this blog

Lalacewar mata a Nijeriya

Zango Ya sayawa Matarsa Dankareriyar Mota