Posts

Showing posts from May, 2012

SA'INSA TSAKANIN KISHIYOYI..KISHI NE KO KWADAYI?

Ganin yadda al'amura ke cigaba da lalacewa ne yasa ni yanke shawarar wannan rubutu don jawo hankalin 'yan uwa iyaye mata bisa wannan babbar matsalar ta kishi domin sanannen abu ne gaduk mai bibiyar kafafen yada labaru na gani ko na karatu irin yadda kullum muke cin karo da munanan labarai na cewar kishiya ta kone yar uwar zamanta da ruwan zafi ko kuma kaji kishiya ta hallaka dan yar uwar zamanta, kai hatta makonnin da suka gabata sai da jaridar aminiya ta bankado wani labarin wata mata wacce don rashin tausayi da karancin imani ta shayar dan abokiyar zamanta man fetur yaron ya sheka har lahira, to ire iren wannan matsaloli da rashin imani yana nan ya zama ruwan dare gama duniya domin ko baka mu'amala da harkokin labaru to na tabbata a unguwar dakake baza ka kasa sanin ko cin karo da kwatankwacin irin wannan matsalar ba awani gidan zaka samu ba zaman lafiya kullum cikin dambace wa ake tsakanin kishiyoyi babu zaman lafiya kullum sai rikici da gaba da juna.  To w

Sarkin Jama’are ya albarkaci wakata - Badariyya meke tsakaninta da AMINU BAGWAI HAR YAYI MATA WAKA?

“Godiya ga mutan Jama’are, Jama’are garin Badariyya!” Wakar da take ta tashe ke nan a sassan kasar nan har ma da kasashen waje. Amma wace ce Badariyya? Wakilinmu ya yi tattaki har zuwa garin Jama’are, inda ya gana da Badariyya, ta yi masa bayani filla-filla, yadda ta hadu da mawaki Aminu Bagwai, wanda kuma ya wake ta. Ga yadda tattaunawar ta kasance: Ki gabatar da kanki ga masu karatu? Sunana Badariyya A Jarma, wacce yanzu aka fi sani da Badariyya Jama’are. An haife ni a ranar 1 ga watan Maris, 1990 a Karamar Hukumar Jama’are da ke Jihar Bauchi. Ko mene ne sanadiyyar haduwarki da Aminu har ya yi maki waka? Lambar wayarsa na nema, da na samu sai na kira shi don ya yi mini karin bayani a kan wakarsa da ya yi ta ta’aziyyar wadanda suka yi hadari a jirgin ruwa, musamman da yake takaddama ta kaure a kan ko hakan ya faru ko a’a. Da na kira shi ne ya sanar da ni tabbas hakan ya faru, a nan na yi masa jaje. Daga nan sai ya tambaye ni ko ina