Lalacewar mata a Nijeriya

in an ce karuwa to za ka ji jama'a suna fassara ta daban-daban. In abin ka tambaya ne, me ake nufi da karuwa? Wani zai ce maka mai zaman kanta, wani ya ce mazinaciyar da duk lokacin da aka neme ta da yin zina za ta yi. Wasu kuma na fassara wacce take gaban iyayenta, amma mai wadannan siffofi da na ambata da 'yar iska. Ma'ana a nan karuwa ita ce wacce ta bar gidansu, 'yar iska kuwa wacce take gaban iyayenta ko da aikinsu daya ne.

Amma ni ina ganin da wacce ta bar gidansu da wacce akan zo a dauke ta a kai ta duk inda aka ga dama a yi zina da ita a dawo da ita gidansu da wacce za ta fita wani lokaci ta dawo in dare ya raba, wata rana ta kwana ta dawo da safe, to a nan fassarar dai shi ne karuwa ce, dukkansu aikin daya ne. In muka faro daga Legas za ka ga karuwanci a wannan jiha yana daya daga cikin manyan sana'o'i a wajen mata. Idan ka duba za ka ga mata a titi tamkar an koro su ne. Wasu a cikinsu ba su da inda za su, sun fito ne ko za su yi dace wani ya dauke su imma ya kai su otel ko wani gida ya yi amfani da su ya biya su, in ta fito wani ya sake dauka.

Makarantun sakandare da jami'o'i, da sauran kwalejoji a birnin Legas sun zama wani sansani ne na karuwai don a Jami'ar Legas har ana samun dillalai maza kawalai wadanda za ka samu ka biya shi ya kawo maka duk irin wacce kake bukata, doguwa ce, mai jiki ce, siriruwa ce, yarinya ce, ko kuwa wacce ta dan manyanta.

Wasu karuwan kuma sukan yi kaura ne daga kauyensu zuwa birni don yawon karuwanci. Kuma a gari irin Legas za ka samu kashi hamsin cikin dari sun yi kudi, sun mallaki gida, wasu kuma har da motoci. Haka idan ka bar Legas ka iso Ibadan, babban birnin jihar Oyo. Za ka samu abin kusan duk daya ne. Da nake zantawa da wani Malami mai suna Sulaiman, ya shaida min cewa da ya je wata unguwa a Ibadan doguwar rigarsa ce kawai ta kwace shi don duk mutumin da karuwan suka gani kiran sa suke yi, amma in sun ga mai dogon riga balle ya rike carbi, sai su ce " Dis wan na Malam libam."

A jihar Benuwe kuwa, wani lokaci ina kallon talabijin sai na ga an nuno jihar ana sharhi a kanta saboda cutar nan ta kanjamau, aka ce ita ce jihar da ta fi kowace jiha a Najeriya ciwon sida. In ko ka duba ko ka laluba za ka ga 'ya'yansu sun fi kowa fita zuwa wasu garuruwa karuwanci, wadanda su har kasashen waje zuwa suke yi. Haka ma yankin Bendel da yanzu ake kira jihar Edo, Inugu da Fatakwal.

Idan muka leka birnin Tarayyar Najeriya, wato Abuja duk da dai ba ko'ina suke ba, amma in ka je inda suke za ka ga abin ma kare ba zai ci ba. Wata rana na tashi da ni da wani kanina daga Wuse II, inda masaukina yake za mu je mu yi siyayya, sai muka je wani wuri da ake kira Kwana shop (corner shop), dama akwai manya-manyan shaguna a wajen. A kan hanyarmu ta zuwa sai na yi ta ganin 'yan mata a gefen hanya suna ta kiran maza, musamman in sun ga mota. Sai ka ga suna rige-rige kowacce sai ta yi "Sis", sai na ga abin kamar wasa. Da abokin tafiyata ya ga haka, sai ya ce bari mu karasa, ai da isa wajen, sai na ga abin ba magana. Za ka ga mata tamkar ana buki ga motoci na alfarma, amma sun zo daukar mata. Da yake wurin ba dakuna za ka ga kowacce ta caba ado ta zo a dauke ta a je a kwana da ita a biya ta.

Kowace irin kabila za ka samu a wajen. Mun fito daga wani shago kenan, sai muka ga ana ta faman kwafsa fada tsakanin wasu karuwai biyu. Ni da ina ce Inyarmurai ne saboda an yi shafe-shafe an zama jazur, ashe Hausawa ne. Sai na ji daya na cewa "Shegiya karuwar Obalande." Sai na fahimci cewa sun ci Legas ne kuma aka zo za a ci Abuja.

Haka in ka je wani wuri da ake kira Mabushi, abin ya kazanta. Don wurin ma da an ga mutum to kawai ba tantama dan iska ne. Wata rana na cewa abokin tafiyata mu shiga babban otel na Abuja Sheraton. Wato wannan wuri in ka shiga za ka ga abu iri-iri. Akwai wani wuri da ake caca mai suna "casino", za ka ga kashi saba'in na matan wurin musulmi ne.

Karuwanci bai tsaya a nan ba. In muka dawo arewacin kasar nan za ka samu akwai abin da yake taimakawa wajen haifar da karuwanci. Na farko akwai talauci da wasu al'adu da aka kirkiro wajen yin aure, saboda su ba a samun damar yin aure sosai. Misali in ka dubi wasu garuruwa irin su Hadeja, Zariya, Kaduna, Kafanchan, Jos da Jalingo za ka samu akwai karancin al'adu, sai dai wasu abubuwan da suka sa wahalar ta zama daya. misali kayan lefe wanda nan kashe kudi yake. Don yanzu ma an samu sabon yayi na yin akwati biyu, uku, har hudu. Sannan ga sadaki mai yawan gaske. Wadannan abubuwan sun haifar da rashin yin aure.

In ka leka Maiduguri, Kano, Kazaure, Katisna da Bauchi za ka samu al'adu suna hana yin aure. Na farko saurayi ya balaga kuma kullum sha'awa tana karuwa masa, yana son yin aure, amma ina, saboda rashin gwamnati adila da shugabanni adilai, ya fada cikin talauci da fatara. Ita kuma yarinya za ka samu ta balaga, ta cika ta batse, ita kullum cikin sha'awa take, tana neman mijin aure ruwa a jallo, amma ba ta samu ba, sun ki zuwa saboda yana zuwa iyaye za su fara tatsan sa. Sai a ce to ka kawo kudin na gani ina so, kudin zance, kayan baiko, kudin gaisuwa. In an zo neman sa rana, shi ma da wani dan ihsani da za a yi, sannan a ce lefe, wanda a talakance za ka kashe dubu ashirin, banda wadannan al'adu da aka yi da farko. Sannan a yanka maka sadaki. Kuma watakila jarinka bai kai dubu talatin ba, sai ka ga an gama bukin ba ka da komai, karshe a shiga wani hali. Sai ka ga an fara samun rashin jituwa. Karshe sai saki ya biyo baya. Ka ga iyayen sun ja mata, don kafin ta sake samun miji sai baba ta gani. Daga nan sai ta fara sauraron kowane irin namiji. Sai ka ga abin da ake tsoro ya faru. Daga nan tana iya barin gidansu ta zama karuwa mai zaman kanta.

Idan ka dubi ma jihar Kano za ka ga ma ana mata kirari mai mata, mai mota, mai Naira! Wannan haka yake. Don in ka je makarantun 'yan mata a Kano sai ka tausaya masu. Misali da za ka je makarantar mata ta Shekara da ke Yakasai, sai ka ce duk 'yan matan Kano ne a wajen, amma abin ba haka bane, don ba ta kai ma sauran makarantun ba, kamar KCC Dala, GTC Goron dutse, WATC, Kulliyatu Turasu, GG Kura da 'yar Gaya. In ka ga abin sai du'a'I, kuma za ka samu duk sun matsu da aure.

Akwai wata budurwa wadda da muke magana da ita sai ta ce min shin za mu yi aure kuwa? Don na ga duk samarin ba sa son maganan aure? Na ce mata suna so, amma ba za su iya ba, saboda iyaye sun dora musu wani abu.

'Yan mata kashi uku ne. Duk wacce iyayenta suka yi nasarar kange ta daga maza, to ta fi kowa son aure, in dai ta balaga. Sannan duk wacce take cudanya da maza ko ba ta zina, in maza suna dan kama ta to son aurenta bai kai ta farkon ba, sannan duk wacce take zina a lokacin da ta ga dama, to za ka samu ba ta cika damuwa da aure ba.

Za ka samu in yarinya ta balaga ba ta samu miji ba, to za ta so namiji ya kamata don ya cire mata sha'awa. Daga nan sai a fara zina da ita har sai ta zama karuwa mai zama a gaban iyayenta. In kuma ana so a taka mata birki, sai ta gudu wajen wani dandali, daga nan ta zama karuwa mai zaman kanta.

Idan ka je Jami'o'i ko kwalejin kimiyya da fasaha za ka samu yawancin mata ba karatun ya kai su ba, sun zo don samun wata dama ne na su yi mu'amala da maza ko za su samu aure, in ba a samu ba, sai ka ga an fara zinace-zinace.

A karshe dai a kasar nan za ka samu wasu wuraren da suka shahara wajen tara karuwai irin Marabar Jos, Gadan Tamburawa, da Gadan Kazaure. In ka shiga Kano wurare kamar Plaza, Gidan Mangoro, Wudil, Fagge, Sabon gari, Kurna da sauransu. Za ka samu iyaye suna turowa a yi musu addu'a a wurin Malamai don 'ya'yansu su sami mazajen aure. In an samu maimakon a yi sai a fara kirkiro wasu abubuwa da za su kori mutum. In ka je Kaduna, Kano, Katsina, Bauchi, Adamawa, za ka rinka samun gida akwai 'yan mata biyar ko uku sun isa aure, amma ba maza. Daga nan sai fara karuwanci don dai a cire sha'awa. In ka je Numan cikin jihar Adamawa za ka ga akasarin gidaje akwai dan shege, saboda arnan wannan gari sun dauki zina tamkar halal.

Wani abu da na lura da shi shi ne, lallai maza sun matsu, saboda lokacin da ake gangamin shari'a a wasu jihohi kuwa za ka ji samari na cewa ai yanzu aure zai sauko, wasu farin cikinsu da wannan shari'a shi ne watakila za su yi aure.

A karshe ina wa iyaye da sauran 'yan mata nasiha cewa in sun sami miji natsattse su aura masa, kar ya zamana ana waige-waige ana neman maiko. Tirmizi ya rawaito cikin littafinsa yana cewa Manzo (sawa) ya ce "Idan kuka yarda da dabi'arsa da addininsa, ya zo muku, to ku aura masa idan ba ku yi haka ba, to za ta zama fitina a bayan kasa da barna mai girma."

Kun ga a nan idan aka tsaya tunanin me ya mallaka, to karshe abin ba zai yi kyau ba. A yanzu za ka ga 'yan mata son aurensu ya fi son wanda za su aura. Allah ya kiyaye mu daga fadawa irin wann

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

Sarkin Jama’are ya albarkaci wakata - Badariyya meke tsakaninta da AMINU BAGWAI HAR YAYI MATA WAKA?

Zango Ya sayawa Matarsa Dankareriyar Mota