Posts

Showing posts from April, 2012

SHARHIN NA MUSAMMAN KAN FIM DIN MALIKA.

Sharhi kan fim xin Malika 1 da na 2 Kamfanin: Saira Movies. Labari/Tsarawa: Maje El-hajij. Manajan shiri: Sani Mai iya. Shiryawa: Nazifi Asnanic. Ba da Umarni: Aminu Saira. Shekarar fitowa: Disamba, 2011 Lokaci Malika 1: Awa 1 da minti 13 da kuma sakwan 45 Lokaci Malika 2: Awa 1 da minti 13 da sakwan 13 Yawan fitowa Malika 1: 32 Yawan Fitowa Malika 2: 26 ‘Yan wasa: Ali Nuhu, Nafisa Abdullahi, Maryam Muh’d, Rabi’u Rikadawa, Jamila Umar, Sadiq Ahmad, Hafsat Sharaxa da sauransu. Labarin Abdulmajid (Ali Nuhu), wani xan jarida mai yin aiki tsakaninsa da Allah ne da matarsa Karima (Nafisa Abdullahi), mai tsananin kishi da zurfin ciki, wanda Malika (Maryam Muh’d), mace marar kamun kai, kuma tsohuwar budurwar Abdulmajid, suka haxa kai da qanwarsa Ummi (Jamila Umar) da mijinta Alhaji Barmo (Sadiq Ahmad), wajen kunna masa wutar rikici da rashin zaman lafiya a gidansa, sakamakon rubutu da yake yi a kan Alhaji Barmo, saboda zaluncin da yake yi, rashin zaman lafiyar da har ya shafi gidan s