Posts

Showing posts from 2011

Lalacewar mata a Nijeriya

Image
in an ce karuwa to za ka ji jama'a suna fassara ta daban-daban. In abin ka tambaya ne, me ake nufi da karuwa? Wani zai ce maka mai zaman kanta, wani ya ce mazinaciyar da duk lokacin da aka neme ta da yin zina za ta yi. Wasu kuma na fassara wacce take gaban iyayenta, amma mai wadannan siffofi da na ambata da 'yar iska. Ma'ana a nan karuwa ita ce wacce ta bar gidansu, 'yar iska kuwa wacce take gaban iyayenta ko da aikinsu daya ne. Amma ni ina ganin da wacce ta bar gidansu da wacce akan zo a dauke ta a kai ta duk inda aka ga dama a yi zina da ita a dawo da ita gidansu da wacce za ta fita wani lokaci ta dawo in dare ya raba, wata rana ta kwana ta dawo da safe, to a nan fassarar dai shi ne karuwa ce, dukkansu aikin daya ne. In muka faro daga Legas za ka ga karuwanci a wannan jiha yana daya daga cikin manyan sana'o'i a wajen mata. Idan ka duba za ka ga mata a titi tamkar an koro su ne. Wasu a cikinsu ba su da inda za su, sun fito ne ko za su yi dace wani

Wani Dan Fulani A Banki

wani baffulatani wai zai wuce ta banki sai ya lura da yadda mutane ke saka katin ATM suna cire kudi gogan naka ba sai ya tsaya ba, yace ikon allah daga ansaka kati sai kudi ya fito? ashe ga hanyar samun kudi asauwake bamusani ba? sai yaje ya sa nasa katin sai computer ta tafi dashi ya jira yaga babu kudi ba kati sai ya fara fada akazo aka tambayeshi sai yace yasa katin sa amma ba kudi ba kati sai aka kai shi customr care suka ce wanne irin kati kasa baba, GOGAN SAI YACE YAKUKE TAMBAYA TA WANNE KATI ZAN SA IDAN BA KATIN DAN KASA BA?9(identity card).

ILLOLIN TABA SIGARI ANAJERIYA

I na mamakin yadda gwamnatin kasar nan ta kware wajan ware da kuma kashe makudan biliyoyi naira akusan kowacce shekara da niyyar inganta harkokin ILIMI, TSARO LAFIYA da kuma TATTALIN ARZIKI akasar nan INDA agefe guda kuma gwamnatin ta toshe kunnuwanta ta runtse ido gami da fatali da fatali da aikin da ya kamata ace tayi, wanda kuma da ace tanayin sa din to da babu ruwanta da fuskantar irin barazanar da ahalin yanzu take fuskanta daga jama'ar kasa dake zargin ta da gazawa wurin inganta musu rayuwa duk kuwa da irin makudan kudaden da gwamnatin ke narkawa da sunan hakan. ABUN da nake nufi da gwamnatin bata aiwatar da aikin ta da ya kamata tayi anan shine idan mun duba gwamnatin najeriya kamar yadda nace tun da farko,gwamnatin tafi bayar da karfi wajan tunkarar matsalolin 'yan kasar da nufin kau dasu ba kuma tare da aiwatar da wani bincike ba, me zurfi dan gano musabbabin dalilin dake kawo wannan matsalar tun daga chan kasa ba domin ta samu damar daukar matakai na ma