SA'INSA TSAKANIN KISHIYOYI..KISHI NE KO KWADAYI?

Ganin yadda al'amura ke cigaba da lalacewa ne yasa ni yanke shawarar wannan rubutu don jawo hankalin 'yan uwa iyaye mata bisa wannan babbar matsalar ta kishi domin sanannen abu ne gaduk mai bibiyar kafafen yada labaru na gani ko na karatu irin yadda kullum muke cin karo da munanan labarai na cewar kishiya ta kone yar uwar zamanta da ruwan zafi ko kuma kaji kishiya ta hallaka dan yar uwar zamanta, kai hatta makonnin da suka gabata sai da jaridar aminiya ta bankado wani labarin wata mata wacce don rashin tausayi da karancin imani ta shayar dan abokiyar zamanta man fetur yaron ya sheka har lahira, to ire iren wannan matsaloli da rashin imani yana nan ya zama ruwan dare gama duniya domin ko baka mu'amala da harkokin labaru to na tabbata a unguwar dakake baza ka kasa sanin ko cin karo da kwatankwacin irin wannan matsalar ba awani gidan zaka samu ba zaman lafiya kullum cikin dambace wa ake tsakanin kishiyoyi babu zaman lafiya kullum sai rikici da gaba da juna.
 To wai shin meke jawo haka ne yan uwana mata? A fahimtar danayi dakuma bincikena na fuskanci ba wai zunzurutun KISHI ke sanya mata masu irin wannan mummunar dabiar abubuwan suke da shukawa ba, akwai rudin zuciya da kuma wadansu dalilai guda biyu da suka hada da kwadayin mallakar gidan da mijin da abun da ya mallaka da ita da 'yayanta  babbar damuwar su idan aka yi musu abokiyar zama bakin cikin su shine itama zata haihu yaran da ta haifa zasu ci gadon dukiyar datake hankoron cinyewa ita da 'yayanta(to a irin hakane rudin zuciya ke sanya su je su aikata wani mummunan abu kan karamin yaro da bai san komai ba, haka nan ta fannin suma Amaren sukan shigo gidan auren su da bakin cikin uwar gidan tare da burin ganin bayanta agidan domin suma su samu damar baje kafa acikin gidan suyi yadda ransu yake so, to ire iren wannan dalilai ne ke hura wutar rikici kaga zama yaki dadi koyaushe aka hadu ana jifan juna da makirci kala kala, Har aje kuma afada halaka to
 yakamata dai yan uwana mata ku farka ku gaggauta sakin wannan turba kuyi koyi da matan Annabi Muhammadu S.A.W wanda suke kishin su bata hanyar fada ko  kone kone ba, ta hanyar kowaccen su tana kishin ganin 'yar uwarta tafi ta kyautatawa Annabi sai itama ta nemo hanyar farantawa mijin nata sabuwa da sauran basu sani ba, dafatan yan uwana mata zukuyi koyi da wadannan salihan bayi

Comments

Popular posts from this blog

Sarkin Jama’are ya albarkaci wakata - Badariyya meke tsakaninta da AMINU BAGWAI HAR YAYI MATA WAKA?

Lalacewar mata a Nijeriya

Zango Ya sayawa Matarsa Dankareriyar Mota