Posts

Showing posts from 2018

Zango Ya sayawa Matarsa Dankareriyar Mota

Image
Fitaccen jarumin fina finan hausa Adam A Zango,  Ya yiwa Matarsa kyautar musamman da sabuwar Dankareriyar mota. Zango ya buga hoton motar kirar  Honda (Continue Discussion) a shafinsa na Instagram inda ya yi wadansu kalamai ma su cike da nuna kauna da Soyayya ga matar ta sa,  a cikin harshen turanci ga abun da yace. "Sabuwar mota kyauta ga matata,  kuma Sarauniyata "

Gabar Ali Nuhu da Zango ta Kare

Image
Ga dukkan alamu an kawo karshen duk wani tashin tashina tsakanin wadannan manyan jaruman Kannywood. Rigimar ta kare ne bayan da Adam A Zango ya fito a ranar alhamis 6 ga satumba ya wallafa sakon ban hakuri da neman Afuwa ga Ali Nuhu a shafinsa na Instagram. Shima Ali Nuhu ya wallafa wakar  Adam A Zango Akan nasa shafin,  wanda wannan ke nuni da cewa sun Shirya. Idan za ku iya tunawa an dauki tsawon shekara guda ana tafka wannan mummunan rikici da ya janyowa mutane da dama rudani da rasa abun yi.    Tuni mutane na cigaba da bayyana ra'ayoyinsu akan wannan batu.