Gabar Ali Nuhu da Zango ta Kare
Ga dukkan alamu an kawo karshen duk wani tashin tashina tsakanin wadannan manyan jaruman Kannywood.
Rigimar ta kare ne bayan da Adam A Zango ya fito a ranar alhamis 6 ga satumba ya wallafa sakon ban hakuri da neman Afuwa ga Ali Nuhu a shafinsa na Instagram.
Shima Ali Nuhu ya wallafa wakar Adam A Zango Akan nasa shafin, wanda wannan ke nuni da cewa sun Shirya.
Idan za ku iya tunawa an dauki tsawon shekara guda ana tafka wannan mummunan rikici da ya janyowa mutane da dama rudani da rasa abun yi.
Tuni mutane na cigaba da bayyana ra'ayoyinsu akan wannan batu.
Comments
Post a Comment