SA'INSA TSAKANIN KISHIYOYI..KISHI NE KO KWADAYI?
Ganin yadda al'amura ke cigaba da lalacewa ne yasa ni yanke shawarar
wannan rubutu don jawo hankalin 'yan uwa iyaye mata bisa wannan babbar
matsalar ta kishi domin sanannen abu ne gaduk mai bibiyar kafafen yada
labaru na gani ko na karatu irin yadda kullum muke cin karo da munanan
labarai na cewar kishiya ta kone yar uwar zamanta da ruwan zafi ko kuma
kaji kishiya ta hallaka dan yar uwar zamanta, kai hatta makonnin da suka
gabata sai da jaridar aminiya ta bankado wani labarin wata mata wacce
don rashin tausayi da karancin imani ta shayar dan abokiyar zamanta man
fetur yaron ya sheka har lahira, to ire iren wannan matsaloli da rashin
imani yana nan ya zama ruwan dare gama duniya domin ko baka mu'amala da
harkokin labaru to na tabbata a unguwar dakake baza ka kasa sanin ko cin
karo da kwatankwacin irin wannan matsalar ba awani
gidan zaka samu ba zaman lafiya kullum cikin dambace wa ake tsakanin
kishiyoyi babu zaman lafiya kullum sai rikici da gaba da juna.
To wai shin meke jawo haka ne yan uwana mata? A fahimtar danayi dakuma bincikena na fuskanci ba wai zunzurutun KISHI ke sanya mata masu irin wannan mummunar dabiar abubuwan suke da shukawa ba, akwai rudin zuciya da kuma wadansu dalilai guda biyu da suka hada da kwadayin mallakar gidan da mijin da abun da ya mallaka da ita da 'yayanta babbar damuwar su idan aka yi musu abokiyar zama bakin cikin su shine itama zata haihu yaran da ta haifa zasu ci gadon dukiyar datake hankoron cinyewa ita da 'yayanta(to a irin hakane rudin zuciya ke sanya su je su aikata wani mummunan abu kan karamin yaro da bai san komai ba, haka nan ta fannin suma Amaren sukan shigo gidan auren su da bakin cikin uwar gidan tare da burin ganin bayanta agidan domin suma su samu damar baje kafa acikin gidan suyi yadda ransu yake so, to ire iren wannan dalilai ne ke hura wutar rikici kaga zama yaki dadi koyaushe aka hadu ana jifan juna da makirci kala kala, Har aje kuma afada halaka to
yakamata dai yan uwana mata ku farka ku gaggauta sakin wannan turba kuyi koyi da matan Annabi Muhammadu S.A.W wanda suke kishin su bata hanyar fada ko kone kone ba, ta hanyar kowaccen su tana kishin ganin 'yar uwarta tafi ta kyautatawa Annabi sai itama ta nemo hanyar farantawa mijin nata sabuwa da sauran basu sani ba, dafatan yan uwana mata zukuyi koyi da wadannan salihan bayi

Comments
Post a Comment