ILLOLIN TABA SIGARI ANAJERIYA

I na mamakin yadda gwamnatin kasar nan ta kware wajan ware da kuma kashe makudan biliyoyi naira akusan kowacce shekara da niyyar inganta harkokin ILIMI, TSARO LAFIYA da kuma TATTALIN ARZIKI akasar nan

INDA agefe guda kuma gwamnatin ta toshe kunnuwanta ta runtse ido gami da fatali da fatali da aikin da ya kamata ace tayi, wanda kuma da ace tanayin sa din to da babu ruwanta da fuskantar irin barazanar da ahalin yanzu take fuskanta daga jama'ar kasa dake zargin ta da gazawa wurin inganta musu rayuwa duk kuwa da irin makudan kudaden da gwamnatin ke narkawa da sunan hakan.

ABUN da nake nufi da gwamnatin bata aiwatar da aikin ta da ya kamata tayi anan shine idan mun duba gwamnatin najeriya kamar yadda nace tun da farko,gwamnatin tafi bayar da karfi wajan tunkarar matsalolin 'yan kasar da nufin kau dasu ba kuma tare da aiwatar da wani bincike ba, me zurfi dan gano musabbabin dalilin dake kawo wannan matsalar tun daga chan kasa ba domin ta samu damar daukar matakai na magancewa misali : al'amarin SARA SUKA abauchi da wasu bata garin matasa keyi suna karkashe junan su wani lokaci ma har da mutanen gari suke hadawa,

YAU kusan shekaru takwas kenan da gwamnatin jihar tun zamanin tsohon gwaMNAN ahmed mu'azu ke ta kokarin kawo karshen wannan matsalar ta hanyar baza jami'an soja acikin garin suna gallazawa duk wanda ya shiga hannunsu amma har yau din nan matsalar sara suka abauchi karuwa take yi, sakamakon gwamnatin bata gano ainahin dalilin da ya jefa su matasan awannan mummunar dabi'ar ba ko kuma ta sani tayi biris ne! wanda kuma dole sai an magance su ne za'a iya samun nasara akan matasan su daina abubuwan dasuke aikatawa na assha,wanda su wannan matsaloli dake damun matasan sune kamar haka:

JAHILCI:da yawa daga cikin matasan basa zuwa makaranta

RASHIN AIKINYI:acikin su kuma akwai wanda sukayi karatu amma basu da aikin yi

TALAUCHI:na uku kuma na karshe shine talauchi dukkansu suna fama da kantar bakin talauchi wanda ke gurbata musu tunani zama 'yan sara suka ko 'yan ta'adda, TO da ace gwamnatin jihar tayi kokarin magance musu wannan matsaloli, ta hanyar tura su makaranta kuma tana biyan su alawus, wanda suka gama ta samar musu aikin yi tana biyan su albashi TO hakika da tayi hakan data magance musu talauchin dake zama sanadin shigar su irin waddanan munanan dabi'u, sannan ne to daga karshe sai tayi amfani da jami'an tsaro wajan kamawa da kuma hukunta duk wani acikin su da ya dawo ya ci gaba da aikata mummunar halayyar, TO DA ba shakka da anyi haka da ansamu sa'ida.

KAMAR yadda, da ace gwamnatin kasar nan ta damu da halin da da kasar dama talakawan ke ciki da sun gano mummunar BARAZANAr da lafiya, tsaro dakuma tattalin arzikin kasar nan tamu ke fuskanta dalilin shigo mana da TABA SIGARI da wasu kamfanonin ketare keyi, da kuma ace wakilcin jama\a suke yi ba wakilcin kawunan su ba da sun gano dakuma dakatar da kashe makudan kudaden da suke barnatarwa sun dawo baya don ceto dumbin 'yan najeriya akalla kashi talatin da biyar cikin dari na yawan mutanen najeriya da suka tsinci kawunansu da tsananta tu'ammali da wannan hayaki me matukar cutarwa ga lafiyar me sha da kuma wanda ke shekar warinta. wani abun takaici kuma kashi ashirin da biyar daga cikin wannan adadi talakawa ne marassa karfi da sai sun fita sun nemo abun da zasu sawa bakin salati, wani kuma zaka ga gani sigarin ce zata lashe rabin samun sa akowacce rana koma fiye da rabin abun da ya samu. yadda misali yana samun naira 350 ne akoacce rana to babu shakka kasafin kudin tabar dazai dadda aranar zai iya kaiwa 150, ko dari biyu, wanda hakika wannan ba karamar masifa bace da hatta tattalin arzikin kasar mu ke fuskantar mummunar barazana ganin cewa kamfanunnukan dake kera wannan sigari din daga ketare suke yinta kuma tabbas daga karshe kudaden zasu kwashe shine zuwa kasashen su yayin da mukuma muka busa kudin mu asararin subuhana. daga karshe bayan barazana ga lafiya da tattalin arziki da gurbata muhalli wannan babbar annoba na matukar gurbata tarbiyyar masu shanta wanda karshe suke karfafawata hanyar komawa shan taba TABAR GANYEN WIWI

wanda hakan shima babbar barazana ce ga hukumomin tsaro ganin cewar yawancin masu aikata munanan laifuka kanyi amfani da tabar wiwin dan gusar da hankulan su tare dayin abun dasukayi niyyar aikatawa na ta'addanci,

AKARSHE NAKE fatan cewar gwamnatin tarayyar najeriya zata farka daga barcin da takeyi dan kawo karshen wannan lamari, ta hanyar da ya dace koma dai ta tsawwalawa kamfanunnukan tabar sigarin kudin haraji yadda zatayi tsada sosai har tafi karfin masu siyan ta dan kubutar da rayukansu da zaman lafiyar kasa da kuma tattalin arzikin mu. DAGA ALIYU DALHATU JAMA'ARE

imel sarkakiya@yahoo.com phone:08094803648

Comments

Popular posts from this blog

Sarkin Jama’are ya albarkaci wakata - Badariyya meke tsakaninta da AMINU BAGWAI HAR YAYI MATA WAKA?

Zango Ya sayawa Matarsa Dankareriyar Mota

Wani Dan Fulani A Banki