Lalacewar mata a Nijeriya
in an ce karuwa to za ka ji jama'a suna fassara ta daban-daban. In abin ka tambaya ne, me ake nufi da karuwa? Wani zai ce maka mai zaman kanta, wani ya ce mazinaciyar da duk lokacin da aka neme ta da yin zina za ta yi. Wasu kuma na fassara wacce take gaban iyayenta, amma mai wadannan siffofi da na ambata da 'yar iska. Ma'ana a nan karuwa ita ce wacce ta bar gidansu, 'yar iska kuwa wacce take gaban iyayenta ko da aikinsu daya ne. Amma ni ina ganin da wacce ta bar gidansu da wacce akan zo a dauke ta a kai ta duk inda aka ga dama a yi zina da ita a dawo da ita gidansu da wacce za ta fita wani lokaci ta dawo in dare ya raba, wata rana ta kwana ta dawo da safe, to a nan fassarar dai shi ne karuwa ce, dukkansu aikin daya ne. In muka faro daga Legas za ka ga karuwanci a wannan jiha yana daya daga cikin manyan sana'o'i a wajen mata. Idan ka duba za ka ga mata a titi tamkar an koro su ne. Wasu a cikinsu ba su da inda za su, sun fito ne ko za su yi dace wani...